Min menu

Pages

Hanya mai sauki da zaka hana ayi adding dinka a group na WhatsApp dole saida izininka.

 Hanya mai sauki da zaka hana ayi adding dinka a group na WhatsApp dole saida izininka.


Hanyar da zaka hana a dameka da tura sako ta WhatsApp ba tare da kayi blocked din mutum ba

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna godiya kuma muna jin dadi kwarai da gaske Allah ya bar kauna.


A yau munzo da hanyar da zaku hana ayi adding dinku a group na WhatsApp dole saida izini.


Kamar yadda muka sani mutane suna damuwa sosai duk lokacinda sukaga an sanya su a wani group na WhatsApp ba tare da saninsu ba wani abin takaicin ma sai kaga kwata kwata mutum baima san mai number da ya sanya shi a group din ba kawai sai tsintar kansa yayi a ciki.


Wani group dinma sai kaga bai dace ace an sanya ka a ciki ba saboda abubuwan da akeyi na shirme da shiririta...


To yau dai wannan abin yazo karshe domin babu wanda ya isa ya sake sanyaku a wani group na WhatsApp dole sai kunga dama kuma kun amince..


Idan baku aminta ba dole saidai su hakura domin babu yadda za suyi daku..


Da farko kai tsaye kuje gurin wasu madanne guda uku da suke sama bayan kun shiga cikin WhatsApp dinku sannan kai tsaye saiku tafi gurin da aka rubuta setting.


Bayan kun shiga gurin da aka rubuta setting saiku tafi  wani guri a kasa da aka rubuta "account"  saiku zabi gurin da aka rubuta privacy bayan ka shiga a kasa za kaga inda aka rubuta group kai tsaye saika shiga.


Zakaga gurare guda uku bayan ka shiga zaka ga gurin da zaka iya barin kowa yayi adding dinka a group ko baka sanshi ba wato gurinda za kaga ansa ALL,  sai kuma daya gurin wanda zaka iya barin sai wanda suke da number ka ne ko kuma kake da number su ne kawai zasu iya sanyaka a group bayan ka amince.


Sai daya gurin kuma inda kaine zaka zabi wanda zai iya yin adding dinka a group din


Daga nan saika zaba shikenan an wuce gurin.

Comments