Min menu

Pages

Dalilin Da Ya Sa Nake Fitowa A Matar Manya A Fim – Jaruma Khadijah Mustapha

 Dalilin Da Ya Sa Nake Fitowa A Matar Manya A Fim – Jaruma Khadijah MustaphaGa duk wanda ya ke kallon jaruma Khadeejah Mustapha a cikin fina-finan da ta ke fito wa, zai ga ta fi fito wa a matsayin matar wani babban attajira, ko kuma mai rike da mulki. don haka ne masu kallon fim su ke kiran ta, da matar manya.


Ganin irin tasirin da sunan ya yi a gare ta, ya sa wakilin Dimukaradiyya ya nemi jin ta bakin ta, akan ya ta ke ji, idan an kira ta da wannan sunan, kuma ita ce, ta ke zabar rol din? ko dai a kan Dora ta ne don ganin ta dace da shi?


Sai ta ce ” To ni ina ganin masu fim din ne su ke ganin na fi dace wa da wannan matsayin da su ke dora ni a kai. Ba ni na ke zabar wa kai na ba, Amma kuma a matsayin ka na jarumi, sai ka duba ka gani, wane rol ne ya kamata ka yi, idan za a ba ka aiki, sabida wani na zuwa, kai a wajen ka ba wani abu ba ne, amma a wajen masu kallo sai ya zama wani abu, don haka, dole sai mutum ya na kiyaye wa” inji ta.


Ta ci gaba da cewa “Amma ni a ra’ayi na, ina son a ba ni rol din da zai kasan ce matar aure a gidan ta, wannan rol din shi na fi so. Amma kuma babu wani rol din da zan ce ba zan fito ba, sai dai idan ya saba wa ka’idar addini na, in dai ya saba wa addini na, to gaskiya ba zan yi shi ba.”


A karshe ta yi kira da jama’a musamman ma masu Kallon fina-finan Hausa cewar “A rinka hakuri da mu, saboda wani lokacin za mu yi abu ba dai-dai ba. Don haka masu kallo, ku-ku ke gani. sai ku rinka yi mana Uziri, da kuma yi mana nasiha. ” a cewar ta.

Comments