Min menu

Pages

'YAN KANNYWOOD BASU YIWA SANI SK RANA BA!

 'YAN KANNYWOOD BASU YIWA SANI SK RANA BA!Wani bawan Allah yace duk da cewa wannan magana ba hurumin nayi magana akai bane, amma sai dai akwai bukatar aja jankalin masu rawankai wanda suke ganin sun samu sana'ar da zasu maida ita hanyar cin abinci har su dinga alfahari dashi


Shirya fina-finai lalatacciyar sana'a ce, wanda ake anfani da lokacin mutum, dazaran lokacinka ya wuce shikenan ka dena anfani za'a jefar da kai


Lokacin da kake da jini a jiki, lokacin da ya dace ka gina rayuwarka dana 'ya'yanka ka basu tarbiya nagari, amma sai kaga mutum yana can yana bautawa 'yan daudu suna anfani dashi suna samun kudade, daga karshe kuma idan jarabawa ta sameshi babu wanda zai taimaka masa


Yanzu don Allah jama'a ku duba, na karanta wani labari a gidan wata jarida akan rashin lafiyar Sani SK, ya jima yana fama da rashin lafiya, harma yayi bidiyo aka yada yana neman tallafin kudin jinya, amma duk cikin 'yan Kannywood an kasa samun mutum daya wanda zai dauki nauyin kula da jinyarsa


Sani SK shekara nawa yayi yana Kannywood? Ko dai basu san halin da yake ciki bane duk da yayi bidiyo yana neman agaji? 

Amma saboda butulci irin na 'yan kannywood suka shashantar da rashin lafiyar 'dan uwansu abokin aikinsu, da Sani SK aka fara gina Kannywood, ya bada lokacinsa, yanzu da jarrabawan rashin lafiya ta sameshi sun kasa daukan nauyinsa, sun gujeshi


Yau inda 'Yan Kannywood mutanen kirki ne ai duk karshen wata koda dari biyar-biyar zasu dinga  hada masa, wanda hakan zai taimaka ya dauki nauyin jinyar rashin lafiyarsa da na iyalansa, cikinsu mutum daya zai iya daukan dawainiyarsa amma abin kunya sun kasa


Daga karshe sai wani 'dan siyasa ne mai suna Malam Inuwa wanda akafi sani da Raba Gardamab bayan ya kalli bidiyon Sani SK yane neman tallafi yayi tattaki har gidansa,  ya kuma dauki nauyin kula da jinyar da Sani SK yake fama dashi


KALUBALE GAREKU 'YAN KANNYWOOD:👇


Abin kunya ne ace 'dan uwanku abokin sana'arku ya jima yana fama da rashin lafiya amma a cikinku an kasa samun wanda zai taimaka masa


Lallai ya kamata duk wani 'dan Kannywood mai hankali wanda shedan bai masa fitsari akai ba ya dauki babban darasi akan abin da ya faru da Sani SK, da ma sauran wadanda suka kare a wulakance cikin jaruman Kannywood


Sana'ar shirya finafinai ba sana'ar kirki bace, ana anfani ne da lafiyarKu da kuma kuruciyarku da kyawun surar jikinku, dazaran wadannan abubuwa sun gushe shikenan anfaninku ya Kare, juji sai ya fiku amfani

Yana da kyau kuyi kokari wajan gina rayuwarku ta hanyar da ta dace ba hanyar banza ba


Allah Ya sauke, Ya bawa Sani SK lafiya Amin

Comments