Min menu

Pages

Ni ba Musulmi ba ne, Amma Na san Annabi Muhammadu Shi ne Mutumin da Yafi Kowa a Duniya Inji Chicharito

 Ni ba Musulmi ba ne, Amma Na san Annabi Muhammadu Shi ne Mutumin da Yafi Kowa a Duniya Inji ChicharitoDuk waɗanda suka san shi saidai su faɗi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi.


Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi.


 A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da ya ke wa Manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.


Duk da ko Chicharito mabiyin Katolika ne, rayuwar Annabi ta matuƙar burgeshi har ya bayyana abinda ke ranshi.


Chicahrito ne ɗan kwallon kafa na farko a ƙasar Mexico da ya yi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya halarci wasan gasar kwallon kafa ta duniya a 2010. An karamashi bayan da yaci kwallaye 7

Abun farin ciki ne da jin daɗi idan kaga wadannan mutanen suna karanta tarihin Annabi kuma sun bayyana kaunarsu gareshi. Allah ya kara tabbatar da mu cikin addinin musulunci da shiriya ta gaskiya.

Comments