Min menu

Pages

A goge shafin sahara reporters ko a dakatar da Facebook a Nijeriya'Yan uwa Musulmi sun bayyana cikin wannan yanayi da suke bayyana kiyayya ga Sahara Reporters 


Jama'ar Musulmi ya kamata mu fara kira ga Gwamnatin Nigeria ta dakile facebook a Nigeria kamar yadda aka yiwa Twitter matukar facebook basu goge jaridar Sahara Reporters ba


Matukar facebook zasu kyale wasu suna amfani da facebook wajen kokarin kunna wutar yaki a Nigeria to mun amince a dakile Facebook a Nigeria domin kasar ta zauna lafiya


Abinda Sahara Reporters suka wallafa zai iya haddasa kazamin yaki a Nigeria, ya zama wajibi Gwamnatin Nigeria ta tashi tsaye ta magance wannan abin


Dole Facebook da Twitter suyi rijista da Gwamnatin Nigeria, Gwamnati ta gindaya musu sharadi, cikin sharuddan ya kasance facebook zasuyi alkawari wajen daukar mataki kan duk wani shafi da yake wallafa abinda zai ruguza mana Kasarmu Nigeria


Muna rokon Allah Ya bawa Gwamnati ikon daukar matakin da ya dace


Allah Ka tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria

Comments