Min menu

Pages

WANI MATASHI YANA SHIRIN FICEWA DAGA MUSULUNCI

 WANI MATASHI YANA SHIRIN FICEWA DAGA MUSULUNCIWannan matashi mai suna Abba yana shirin fita daga addinin Musulunci, yace tsawon rayuwarsa bai ga wani amfani a cikin Musulunci ba


Yace ya bada wasu kwanaki kalilan idan har Musulmi basu nuna masa wani abin amfanarwa ba a cikin Musulunci, kuma idan Gwamnatin Nigeria bata bashi mukami ba to zai fita daga addinin Musulunci, kamar yadda ya bayyana hakan cikin bidiyo a shafinsa na facebook


Bayanin shafinsa na facebook ya nuna cewa 'dan jihar Jigawa ne, a cewarsa wai ya karanta Qur'ani gaba daya amma bai gane amfanin Musulunci ba sai tashin hankali


A yadda yaron yake managa kamar 'dan kwangilar yahudawa ne ko kuma yana da tabin hankali, ko kuma ya zama "Atheist" masu sabon addinin babu Allah, amma nafi fahimtar kamar yana da tabin hankali ne, domin yace dole Gwamnati sai ta bashi mukami kafin ya cigaba da zama a Musulunci, wannan furucin nasa yayi kama da wanda bai da lafiyar kwakwalwa


Idan akwai wadanda suka sanshi suka san 'yan uwansa  to ya kamata ayi saurin ankarar da 'yan uwansa su dubi abinda yaron yake wallafawa a shafinsa na Facebook, idan ya tabbata bai da lafiya su hanashi hawa facebook su nema masa magani


Allah Ka shiryar dashiComments