Min menu

Pages

Ni ba Nnamdi Kanu bane dan haka babu ubanda ya isa ya kamani inji Sunday Igboho

 Niba Nnamdi Kanu bane dan haka babu ubanda ya isa ya kamani inji Sunday Igboho
Shahararren dan tawayen yankin Yarabawannan wato Sunday Inugbo ya barana safiyar ranar Asabar yana cewa shi fa ba Nnamdi Kanu ne ba da zai bari a kama sa kamar yadda ya bayyana Mr Sunday Igboho ya ce.


“Wannan abin da nake yi ina yinsa ne don kwatar wa yankinmu na yarabawa yancin cin gashin kansa daga Najeriya ba wai ina yi ne don bukatun kaina ba saboda haka babu gudu babu ja da baya dole ko ana so ko ba’a so sai mun kafa kasar mu” in ji shi kamar yadda ya bayyana a firar sa da wata kafar yada labarai mai suna Yoroba News.

 

Idan ba’a manta ba dai a karshen makon da ya gabata ne hukumomin Najeriya suka kama dan’uwansa mai fafutukar kafa kasar Biafra wato Nnamdi Kanu, inda shi ma kansa Sunday Inogbon suka ayyana nemansa ruwa a jallo sakamakon yunkurin da yake yi na tayar da zaune tsaye a kasar, da kuma makaman da aka samu a samamen da aka kai a gidansa.


Muna fatan Allah ya yi mana maganin wadannan mutane masu son tayar da fitina a kasar nan ameen.

Comments