Min menu

Pages

Tsohon Gwamnar Jihar Borno Kashim Bukar Shetima Yayi Magana Mai Zafi Akan Gwamna Babagana Zulum

 Tsohon Gwamnar Jihar Borno Kashim Bukar Shetima Yayi Magana Mai Zafi Akan Gwamna Babagana Zulum.A Cewarsa; Gwamna Zulum matsalarshi ba kudi bane... Dalilai?


Nabashi Shugaban kwalejin harkar noma amma bai gina gidan kanshi ba.


Nabashi kwamishina na gina gine wanda har saida nasa kudi N20bn amma har yagama bai gina gida ba, Yan zaune a gidan gadonsu a Maiduguri.


Nayi mamaki matuka, Wanda saida nakaimai ziyarar bazata domin na tabbayarda gaskiyar lamarin, Amma sai nasameshi a gidan gadonsu.


Mutane 32 Yan jam'iyar APC sunason suhau kujera na bayan na sauka, Amma saidai kawai nayi dariya saboda nariga na zabi wanda zai gajeni, kuma wanda baya cin hanci da rashawa wato Zulum, Shine mutumin daban taba gani ba a rayuwata.


Namai magana akan ya gajeni ya zama Gwamna amma yaki saidama ya gudu yaje makka.


Daya dawo saina kara tuntubanshi, Sai yacemun baida kudin dazai sai form ma ballantana na Campaign.


Nida kaina nasiyamai form Sannan na samar da kudin da ayi campaign baki daya.


A yau ina mai matukar farin ciki na samama Borno gwamnar da babu kamarsa.


Comments