Min menu

Pages

Na Yar Da Ƙwallon Mangwaro Yanzu Zarah Zan Aura Na Haƙura Da Auren Hadiza Kabara Dama Ba Sa'ata Ba Ce, Inji Nabraska

 Na Yar Da Ƙwallon Mangwaro Yanzu Zarah Zan Aura Na Haƙura Da Auren Hadiza Kabara Dama Ba Sa'ata Ba Ce, Inji NabraskaShahararren ɗan wasan Hausan nan wato Mustapha Nabraska, ya bayyana cewar yanzu ya fasa auren Hadiza Kabara.


Nabraska ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta Instagram, inda ya sanya hotonsa da jaruma Zarah Diamond, tare da cewar ta kwantar da hankalinta...


"Zarah ƴar halak ki kwantar da hankalinki, nima na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda, sakamakon rainuwa da alkhairi, dama ba sa'ata ba ce (Hadiza Kabara), rigima ta ce." Inji Nabraska


A kwanakin baya ne dai jarumin ya bayyana aniyarsa ta ƙarin mace ta 3 da jaruma Hadiza Kabara, kamar yadda ya bayyana a wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da shi

Comments