Min menu

Pages

DA DUMI DUMINSA WATA KOTU A AMURKA TA BADA UMARNIN A KAMO ABBA KYARI

DA DUMI DUMINSA WATA KOTU A AMURKA TA BADA UMARNIN A KAMO ABBA KYARI
Yanzu-yanzu babbar kotu dake Amurka ta bai wa hukumar bincike ta FBI umurni data gaggauta cafke Abba Kyari domin mika shi zuwa Amurka don gudanar da bincike kan shi


Wata babbar kotu dake California ta kasar Amurka ta bai wa hukumar bincike ta FBI umurnin kamo mataimakin Kwamisshinan 'yan Sanda na kasa Abba Kyari mai yaki da 'yan ta'adda domin mika shi zuwa kasar Amurka don amsa tambayoyi akan laifin da ake zargin sa na kar6an cin hanci da rashawa daga hannun shahararren dan damfarar nan Huspuppi. 


Wannan na zuwa ne bayan da Huspuppi ya bayyana cewa ya bai wa Abba Kyari cin hanci domin ya kama masa wani dan uwan sa damfara dake nan Najeriya wanda ya yi barazanar hana shi damfarar wani mutun dan kasar Qatar $1.1milion.


Shin wane fata kuke yi wa Abba Kyari ne?


Comments