Min menu

Pages

BANKUNA ZASU CI GABA DA BIYAN KUDADE GA MASU CIN GAJIYAR SHIRIN SPW

 BANKUNA ZASU CI GABA DA BIYAN KUDADE GA MASU CIN GAJIYAR SHIRIN SPW 

 


Bankunan Najeriya da aka zaba don Shirin Ayyuka na Musamman na Mutum 774,000 sun fara biyan kudade ga wadanda suka ci gajiyar shirin ayyuka na musamman dukkan kudaden da suka rage kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta umarta.

Jerin jahoji da sukafi yawan masu cutar kanjamau (HIV) a kasar Nigeria

Bankin Access, Fidelity da FCMB a cikin watan Yuni sun fara biyan N40,000 ga mahalarta wadanda tun farko suka fara biyan N20,000 da N60,000 ga mahalarta wadanda ba su karbi Stipend na farko, na biyu da na uku ba.


 Ministan Jiha, Kwadago da Aiki, Mista Festus Kayemo a cikin wata sanarwa daya fitar, ma'aikatar ta gano badakala ake a cikin tsarin, kamar asusun da bai dace da BVN ba, asusun da yawa da ke dauke da BVN guda daya, da dai sauransu don haka ya umarci Bankunan da ke lura da tsarin da su gyara dukkan matsalolin da suka shafi hakan sannan su biya kowa kuɗaden Su.


 

Sauran bankunan da suke lura da tsarin kamar UBA, Heritage Bank da sauransu, sun fara biyan N60,000 ga mahalarta bayan warware matsalolin.


A matsayin cigaba da  shirin Fitar Yan Najeriya daga talauci akwai shiri na Musamman na Fadada Ayyukan Jama'a, gwamnatin tarayya a farkon watan Yuli ta sanar da shirinta Na horon kasuwanci wanda zai baiwa mahalarta damar yin amfani da damar su na watanni 3 Stipend.


Kakakin hukumar kula da samar da aiyuka ta kasa (NDE), Edmund Onwuliri, ya bayyana cewa za a gudanar da horon ne a kowane yanki na Senetorial Zones da Abuja FCT, ya kuma kara da cewa ana saran mahalartan za su samu dabarun da suka dace da zai ba su damar gano  hanyoyin sarrafa ƙananan kasuwancin kansu bayan sun fita daga tsarin ESPW.


Rahotanni a fadin tarayyar sun bayyana cewa wasu Jihohi da Yankunan Senetorial sun kammala Horon yayin da har yanzu ba a fara ba a Wasu Jihohin da gundumomin Senetorial, cikin tsarin akwai Wanda aka basu tallafin 10,000 sai kuma Wanda za suyi kar6i horo a 6angare daban daban Wanda suma tini an biya Su alawus din kar6an horo 6000.


Allah ya tabbatar da alkhairi Ya Kara daukaka Mana gwamnatin Shugaba Buhari tare da sauran Mukarraban Sa, Allah yaci da Yan baya.


                   

Comments