Min menu

Pages

KU KARE KAN KU DA CIZO DA KUMA DANƘO INJI MASARI

 KU KARE KAN KU DA CIZO DA KUMA DANƘO INJI MASARINaga Wani Faifan Bidiyo yana yawo, Inda cikin shi na Jiwo Gwamnan Jihar Katsina Yana Sako Wasu Maganganu, Wanda jinsu a bakin Gwamna Mai ci Bababn Abun Kunyane, Sannan Abun takaicine aji Gwamna Yana irin wannan Maganganu.


A Cikin Faifan Bidiyon Naji Gwamnan Yana Ambata, Jama'a Su kare Kawunansu koda Cizo ne, da kuma Bakan Danƙo! Domin Rashin Tausayi da kuma Rashin iya Shugabanci na Al'umma.


Mutunenn da Suke Ɗauke da Muggan Makamai, Amma Sune za'a Kalli Idanun Talakkawa Ace Idan Sunzo Suje su Cije su, domin kada ace sun kasa.


Mutanen da Idan suka tashi Zuwa, suke Ɗauko Garken Babura Su shiga Gari, Sune Gwamna Zaice ka Samu Bakan Danƙo ka Kare kanka Daga su! Gaksiya Gwamna Aminu Bello Masari Bashida tausayi, Kuma Shugabancin Jama'a Bai Kamaceshi ba, domin Maganganun sa basuyi kamada Maganganu Shugaban Al'umma ba.


Idan Bazaka iyaba, kasauka Kawai, Amma Bawai sai Kazo karinga yiwa mutane magana, wadda Batada Ma'ana ba, Domin Magana ake ta Rayuwa da kuma Dukiya Bawai Magana ake ta Ɓarayin Kaji ba.

Comments