Min menu

Pages

A Biyani Diyyar Miliyan 500 Kan Shigo Min Gida Da Akayi, Inji Sunday Igboho Ga Gwamnatin Tarayya

 A Biyani Diyyar Miliyan 500 Kan Shigo Min Gida Da Akayi, Inji Sunday Igboho Ga Gwamnatin TarayyaMai iƙirarin kafa ƙasar Yarbawa ta Oduduwa, Sunday Igboho ya nemi gwamnatin tarayya ta biya shi diyyar naira miliyan 500.


Hakan ya fito ne ta bakin Lauyansa Yomi Aliyu, inda ya bayyana cewar ya kamata gwamnati ta biya Sunday Igboho saboda cin zarafin da aka masa na shiga gidansa ba tare da sanar dashi ba da kuma izini.


"A yayin ziyarar, an lalata motocin alfarma biyu na Sunday Igboho kuma an kwashe masa kuɗaɗe da wayoyi."


"Babu wani makamai da aka samu a gidan  Sunday Igboho, sharrin DSS ne kawai da suka ga basu samu makami ko ɗaya ba, shine suka ƙwace na ƴan sandan dake baiwa Sunday Igboho kariya suka nuna." Inji Lauya Yomi

Comments