Min menu

Pages

KIRA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MATA NA DUNIYA DA SU DUBI HALINDA MARYAM YAHAYA TAKE CIKI SU BI MATA HAKKINTA

 KIRA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MATA NA DUNIYA DA SU DUBI HALINDA MARYAM YAHAYA TAKE CIKI SU BI MATA HAKKINTAJaruma a masana'antar Hausa film Maryam Yahaya karamar yarinya ce, kafin shigarta Hausa film tana tallen kayan koli anan unguwarsu dake jan bulo a birnin Kano, tana kuma soya awara a kofar gidansu, suna rufawa kansu asiri da iyayenta, wanda suke masu karamin karfi ne, wato talakawa abin tausayi


Lokacin da aka shigar da yarinyar nan wasan hausa film tudun kirjinta bai gama girma ba, ma'ana bata gama zama cikakkiyar balagaggiya ba, da mutuncinta da komai, da farko Mahaifinta bai so ba, yaudaransa akayi aka jefa 'yarsa wasan kwaikwayo


Abokan sana'arta bayan sun ruguza mata rayuwa, sun kawota gidan iyayenta sun jibge a gida, yanzu ko ziyara duba halin da take ciki basa yi, sun kyamaceta


Wannan cin zarafi ne da keta hakkin rayuwar mata dangin rauni, ba a haka 'yan Hausa film suka dauketa a gidan Mahaifinta ba, Mahaifinta bai da karfin daukar Lauyoyin da zasu kwata mata 'yanci a biyata diyya, tunda sun kashe mata rayuwa


Muna kira ga hukumomin Gwamnati da manyan kungiyoyin kare hakkin yara mata su kawo dauki wa Maryam Yahaya, a taimaka wajen kwato mata hakkinta da na iyayenta


Muna izna ga sauran 'yan mata da suke sha'awar wasan kwaikwayo, ku gaji Hausa film babu alheri a ciki ko kadan, sai da na sani marar amfani


Yaa Allah Ka bawa Maryam Yahya lafiya, Ka yafe mata, Ka bada ikon kwato mata hakkinta Amin

Comments