Min menu

Pages

Shin kunsan halinda Maryam Yahaya take ciki?

Shin kunsan halinda Maryam Yahaya take ciki?Duniya makaranta

Daga Datti assalapy

'Yar wasan kwaikwayo a masana'antar Hausa film Maryam Yahaya tana fama da matsanancin rashin lafiya kusan watanni uku kamar yadda kamfanin jaridar Dokin Karfe TV ta ruwaito


Kafin wannan rubutun, nima na gudanar da nawa bincike daga wasu amintattu na da suka san sirrin masana'antar hausa film, tabbas Maryam Yahaya tana fama da jinya wanda bai cancanta a bayyana irin jinyar dake damunta ba


KIRA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MATA NA DUNIYA DA SU DUBI HALINDA MARYAM YAHAYA TAKE CIKI SU BI MATA HAKKINTA


Tsakanina da Allah naji tausayin yarinyar nan, an yaudareta an cuceta an tarwatsa rayuwarta an kaita an baro


Kullun ana yiwa yaran nan nasiha da fadakarwa suyi hankali da duniya, amma saboda jiji da kai suna jin tamkar kasa ba zata iya daukarsu ba, suka rena kowa, ko a yanzu duniya ta koya mata karatu


Lokacin da Maryam Yahya ta tashi shiga hausa film Mahaifinta bai so ba sam, amma haka aka hada baki da wasu lalatattu suka yaudari mahaifin yarinyar ba don yana so ba, gashi sun tarwatsa masa rayuwar 'yarsa sun gudu


Yanayin da Maryam Yahaya ta tsinci kanta a yau sanadiyyar shiga hausa film inda Mahaifinta yana da hali da an bashi shawara ya dauki manyan lauyoyi su buga shari'ah da wadanda suka zalunci 'yarsa


Allah duk wanda yake da hannu a sanadiyyar tarwatsa rayuwar wannan yarinya Allah Ka tarwatsa rayuwarsa shima


Daga karshe muna fatan Allah Ya saukaka wa Maryam, Allah Ya sa jinyar ya zama kaffara a gareta Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Comments