Min menu

Pages

Ka bewa yan Nijeriya damar rike bindinga ko na maka ka a kotu cewar wani lauya

 Ka bewa yan Nijeriya damar rike bindinga ko na maka ka a kotu cewar wani lauya
Babbar Magana: Zan maka Buhari kotu idan bai ba Yan Najeriya damar rike AK47 ba, Inji wani Lauya


Wani mai fafutukar kare hakkin Dan adam Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya sha alwashin maka shugaban Kasa Muhammadu Buhari kotu matukar bai baiwa Yan Najeriya damar rike AK47 don kare kansu. 


Omirhobo, a wata wasika da ya aika a ranar 8 July, 2021, inda yayi mata laqabi da "Neman bada damar sayen bindiga kirar AK47 tare da harsashi."


Ya bukaci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya amince ga dukkanin Dan kasa ya mallaki bindiga kirar AK47 don kare kansa da gidansa da iyalansa harma da kayayyakinsa kan Yan ta'adda.


A lokacin da yake zantawa da Jaridar Daily trust cewa yayi ya shirya tsaf don tunkarar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kotu nan da yan kwanaki kadan masu zuwa.


Ya kara da cewa "Ni dan Najeriya ne mai kishin kasa, kuma lafiyayye wanda yasan mai yakeyi, Ni mutum ne mai kyakykyawan dabi'a an sanni sama da shekaru biyar ban taba aikin ta'addanci ba."Comments