Min menu

Pages

INA NEMAN MIJIN AURE ƊAN WANKA KAMAR TSOHON SARKIN KANO MALAM MUHAMMADU SUNUSI I|

INA NEMAN MIJIN AURE ƊAN WANKA KAMAR TSOHON SARKIN KANO MALAM MUHAMMADU SUNUSI I|Fitacciyar mai amfani da shafukan sadarwa na zamani musamman shafin Facebook, kuma malama a jami'ar jihar Kaduna (KASU), Bilkisu Sani Yero wacce aka fi sani da Arewa Queen, ta yi addu'a akan Allah ya bata mutumin da ya iya kwalliya tamkar tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.


Arewa Queen da ta ke koyarwa a sashen nazarin halayyar ɗan adam a jami'ar ta KASU, ta bayyana hakan ne a shafinta na facebook, da yammacin yau Talata, inda masu bibiyar ta a shafin su ka tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.


Bisa al'adar ƙasar Hausa dai namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure.


Amma sakamakon juyin zamani da ya zo da abubuwa masu yawa da sunan wayewa, domin mace kan iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta.


Haka kuma ba wannan ne karon farko da mace ke bayyana fatan samun namiji mai wata dabi'a ko siffata ta fitattun mutane ko kuma so bayyana kai tsaye shi fitaccen mutumin su ke so. Domin ko a ɗan kwanakin nan sai da aka samu wata budurwa tana furucin kafatanin mazan duniya babu wanda ta ke so kamar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Comments