Min menu

Pages

Ina Mamakin yadda Yan Najeriya suka Zabe ni duk da ni bamai kudi bane>>Inji Shugaba Buhari

 Ina Mamakin yadda Yan Najeriya suka Zabe ni duk da ni bamai kudi bane>>Inji Shugaba Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, yace yana mamakin yadda yan Najeriya suka karbeshi Kuma suka zabe shi "duk da shi bamai kudi bane".


Shugaba Buhari ya bayyana haka a lokacin da yake jaddada kudirin shi na yima kasar aiki, iya iyawar sa, tare tunani  akan ziyarar daya kai ga Jahohi 36 a lokacin gangamin yakin neman Zabe na Shekarar 2019.


Maganar shi "yawan mutanen da suka futo domin gani na a lokacin, wasu sun shafe tsawon awanni 10 a cikin rana, yafi karfin abinda wani zai saya ko ya tilasta. Kawai suna so suga waye Buharin nan. Al'umma na Mamakin ya akayi Yan Najeriya suka karbeni duk dani bamai kudi bane. Ni kaina Ina mamakin haka, Naga ya zama dole inyiwa Najeriya da Yan kasar ta aiki, iya iyawa ta".

Shugaba ya kara dacewa, Yan Najeriya su yiwa kansu murna cewa har yanzu ana nan daya, duk da irin Matsalolin dake addabar kowa da kowa.

Comments