Min menu

Pages

Igboho ya Maka Gwamnatin Tarayya Kotu, ya bukaci a sakar masa yaranshi

 Igboho ya Maka Gwamnatin Tarayya Kotu, ya bukaci a sakar masa yaranshiChief Sunday Adeyemo Wanda akafi sani da Sunday Igboho, yaje Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya dake Abuja, domin a sakar mashi mataimakan sa, Wanda Hukumar Yansandan Farin Kaya ta DSS suka kamo a gidan sa, dake yankin Soka ta Ibadan a ranar 1 ga watan Juli.


Babban Lauyan dake kare masu Neman kafa kasar Yarbawa Zalla Chief Yomi Aliyu SAN, ya Shaidawa wakilin Jaridar Punch a wayar salula cewa, a ranar Alhamis ya kai karar a Babbar Kotun dake Abuja, domin sakin mutum 13 da aka kama mashi.


Lauyan bai bayarda bayanin yanayin yadda aka kai karar ba, amma Mai Magana da Yawun Igboho, Olayomi Koiki ya bayarda sanarwar a ranar Laraba cewa, DSS basu bari Lauyoyin Igboho sunga mataimakan ba, dake tsare cikin ofishin su.


A lokacin da aka tambaye shi, akan matakin da zasu dauka domin ganin an sake su, Aliyu yace sun kai kara a Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya dake Abuja akan bayar dasu beli.


DSS dai sun shiga gidan Igboho da Misalin Karfe 1:30 na dare a ranar 1 ga watan Juli, inda suka kashe Mataimakan shi guda 2 tare da kama mutum 13, inda aka kama Harsashi da kayan tsafe-tsafe.


Amma Igboho yaki amincewa da kayan, Yana mai cewa DSS suna so su Shafa masa bakin fenti.

Comments