Min menu

Pages

HATTARA DAI "YAN UWA MATA ABINDA YA SAMU WANNAN BUDURWAR KADAI YA ISA KU NUTSU

 HATTARA DAI "YAN UWA MATA ABINDA YA SAMU WANNAN BUDURWAR KADAI YA ISA KU NUTSUAkwai wata yarinya da ta ke yin karatu a wata college anan kano sai suka hadu da wani kyakykyawan saurayi a collagen nan suka shiga soyayyah ta ban mamaki


Sai da ta kai kowa ya san da soyayyar su tun daga makaranta zuwa kan kawayenta har zuwa gidan su yarinyar da 'Yan unguwarsu duk sun San shi domin wani Lokacin in yaje unguwar su yarinuar tun safe sai dare yake tafiya


Maza da mata abokanan karatunta sun bata shawarar ta rabu da wannan saurayin nata ta tsaya ta yi karatu amma ina soyayyah ta rufe mata ido Sam taqi yarda domin duk Wanda ya yi mata nasiha sai ta fadawa saurayin nata domin gani take yi kamar Hassada ake yi musu


Ana haka har shedan ya shiga tsakaninsu suka yi abinda bai dace ba bayan wani Lokaci sai saurayin ya fara canjawa budurwar tasa fuska ya dena kulawa da ita nan fa ta damu ta shiga damuwa a takaice sai da karatun ya gagareta saboda tsananin damuwa


Shi kuma saurayin sai yaje ya samu wata kawar budurwar tasa ya tsarata ya aureta nan ma ita tsohuwar budurwar tasa sai da ta kwanta a asibiti saboda tashin hankali ta fita daga kamanninta ta zama wata iri daban


Shi tsohon saurayin ya ce bazai auri matar da yasan jikinta tun kafin yin aure ba don haka ya qi aurenta duk da soyayyar da ta yi masa amma wannan shi ne sakamakonta


Wannan dai babban darasi ne ga mata akan su kiyayi bin saurayin shawo Mata Ku kula Ku yi aiki da Lura Ku dena daka ta bin son zuciya Allah ya sa mu fahimta Allah ya tsare mu da bin hudubar iblis.Comments