Min menu

Pages

Hatsarin Mota: Shugaban Soji ya jajantawa wanda Lamarin ya shafa a yankin Arewa Maso Gabas

 Hatsarin Mota: Shugaban Soji ya jajantawa wanda Lamarin ya shafa a yankin Arewa Maso GabasBabban Hafsan Sojin Kasar nan Laftanar-Janar Farouk Yahaya, ya jajantawa Sojojin da hadarin Mota ya rutsa dasu a ranar 8 ga watan Juli a Garin Kuturu, dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.


Sojojin dai suna kan hanya zasu kai dauki a lokacin da hatsarin ya afku.


Abin bakin ciki, daya daga cikin motocin dake dauke da sojojin ta sauka daga kan hanya, wanda hakan ya janyo hatsarin.


Sojoji 9 da suka samu raunuka a hatsarin, a halin yanzu suna Asibitin Sojoji suna karbar Magani.


Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami'in Hulda da Jama'a na Rundunar Soji Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, inda yace babu mutuwa a hatsarin.


Janar Yahaya ya yabawa Jami'an akan irin kokarin su nakai daukin gaggawa, ya kuma bukace su da su cigaba da kai daukin gaggawar a duk lokacin da aka bukata.

Comments