Min menu

Pages

GASKIYAR BATU:- Wai Da gaske Kwankwaso Na Shirin Komawa Jam’iyya Mai Mulki Ta APC??

 Wai Da gaske Kwankwaso Na Shirin Komawa Jam’iyya Mai Mulki Ta APC??Jaridar Politics Digest ta rawaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kano na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.


Jaridar ta bayyana cewa, Kwankwaso ya tattauna da jagoran APC, Bola Ahmad Tinubu cikin sirrri a kasar Saudi Arabia sannan yana tuntubar masu kusoshin jam’iyyar ta APC.


Sannan akwai wasu gwamnoni na APC dake muradin ganin Kwankwaso ya dawo jam’iyyar ta APC da suka hada da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar da Mohammed Bello Matawalle na jihar Zamfara wanda ya sauya sheka a ranar Talata.


Idan labarin hakan ya tabbata, Kwankwaso zai sauya sheka da dubban magoya baya ciki har da dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2019, Abba Gida-Gida da mataimakinsa, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo.


To sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun musanta labarin inda suke bayyana cewa darajar Kwankwason ce tasa kowanne bangare ke son ya shigo jam’iyyar.


Haka kuma babu wata sanarwa daga bangaren Kwankwaso ko APC na shirin Karbar jagoran na Kwankwasiyya cikin jam’iyyar.

Comments