Min menu

Pages

DA DUMI-DUMI | Nnamdi Kanu ya nemi a zauna lafiya tare da hakuri da juna a Najeriya.

 DA DUMI-DUMI | Nnamdi Kanu ya nemi a zauna lafiya tare da hakuri da juna a Najeriya.Shugaban kungiyar 'yan tawayen nan ta (IPOB) masu rajin kafa gwamnatin Biafra, Mazi Nnamdi Kanu, ya fara kira da hadin kai da kuma hakuri da juna a Najeriya daga can inda yake tsare a gidan gyaran hali.


Lauyan dake kare shugaban 'yan tawayen, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana hakan yau a shafin sa na Twitter, inda yace ya shafe sa'o'i 4 tare da Namdi Kanu suna tattaunawa aagidan gyaran hali.


"Kanu yana cikin farin ciki, yana mai neman a shawo kan wannan matsala nan bada dadewa ba, ya kuma jadda muhimmancin hadin kai da hakuri da juna a dukkan bangarori." Inji Lauyan sa Aloy Ejimakor.

Comments