Min menu

Pages

Duk Namijin Kwarai Yana Son Jin Wadannan Kalmomin Daga Bakin Matarsa:

 Duk Namijin Kwarai Yana Son Jin Wadannan Kalmomin Daga Bakin Matarsa:Mata ga wasu kalmomin da babu wani namijin da baya so yaji matarsa ta furta mata su sai dai namijin da bai san darajar soyayar aure ba.

Yana da kyau a kalla duk wata mace tayi kokarin furtawa mijinta akalla kalma guda daya duk rana.

Hakan yana da matukar tasirin da zai inganta Zamantakewar auren su.

Ga wadannan kalmomin kamar haka:

1: Ban taɓa danasanin auren ka ba.

2: Nayi sa'ar samun miji.

3: Ina alfahari da kai.

4: Na yarda da kai 100 bisa 100 mijina

5:  Na gode.

6: Allah Ya ƙara buɗi.

7: YI haƙuri.

8:Na tuba.

9: Ka ƙara hakuri dani

10: Ka sanar dani abubuwa da dama a rayuwata. 

11: Da duk maza kamarka suke da mata sun huta.

12: Kalamanka kawai suke sani tsuma.

13: Ka shagwaɓani da soyayya

14: Ina godiya da irin ɗawaniyar da kake yi damu.

15: Soyyya da kaunar da kake nuna mini sune suka ɗaukaka matsayina

16: Ina murna idan naga ko naji ka kyautatawa wasu.

17:  Dole ke sa nake nesa da kai.

18: Ina kara sonka a kowani daƙiƙa.

19: Kaine mutuncina.

20: Ko a Aljanna dakai nake burin rayuwa na har abada.


Da fatan zaku yi amfani da su ta hanyar data dace, da kuma lokacin daya dace.

Comments