Min menu

Pages

Babbar Magana: Shugaban Karamar hukumar Gwaram dake Jigawa ya baiwa karuwai wa'adin su bar garin

 Babbar Magana: Shugaban Karamar hukumar Gwaram dake Jigawa ya baiwa karuwai wa'adin su bar garinShugaban Karamar hukumar Gwaram dake Jahar Jigawa ya sanarwa karuwai dake zaune a yankin dasu gaggauta barin garin, wadda kuma ta shirya da aure tana iya turo sunanta dana saurayita a cikin kwana Talatin.


Karuwan da ba Yan asalin Jahar bane su gaggauta komawa Jahar su.


Wadanda kuma Yan asalin Jahar ta Jigawa ne suna iya turo sunan su tare dana samarinsu don daura aure nan da kwana Talatin.


Karamar hukumar ta shirya tsaf don daukar nauyin duk wadda zata bar karuwanci tayi aure.


A wani tattaunawa da sukayi da wasu wakilan yankin Sara, wata babbar kasuwa ce data ke ci duk sati a Karamar hukumar, Abubakar ya gayawa masu sana'ar karuwanci a gurin dasu tattara sunayen su zuwa Ofishin Karamar hukumar kamin ranar da aka saka.


Ya kuma ce an baza jami'an tsaro da su tura wacce suka kama ba Yar asalin Jahar ba zuwa garinsu.


Ya kuma sanar da rufe dukkanin gidan wasanni da badala (Club) a fadin jahar.


Abubakar yace anyi hakane don rage yawan bata gari a karamar hukumar.


Comments