Min menu

Pages

Kwankwaso yace zai koma APC shida jama'arsa amma sai an yarda da wadannan sharudan

 

Kwankwaso yace zai koma APC shida jama'arsa amma sai an yarda da wadannan sharudanWani daga cikin magoya tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya a zauren majalissar dattawan Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun ce matukar jam’iyyar APC na son jagoran nasu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya koma cikinta to lallai babu shakka sai idan ta cika wasu ka’idoji kamar haka.


Na farko dole sai idan jam’iyyar za ta bawa Sanata Kwankwason tikitin taka takarar kujerar Shugabancin kasar nan a zaben 2023 mai zuwa.Na biyu wajibi ne jam’iyyar ta rushe shugabancinta na jihar Kano, a sake zabe sanann ta damka ragamar gudanar da jam’iyyar a siyasance ga hannun jagoran nasu wato Rabi’u Musa Kwankwaso.


a cewarsu matukar jam’iyyar ta amince za ta bi wadannan ka’idoji da suka gindaya mata to babu shakka jagoran nasu zai dawo cikin jam’iyyar ta APC.


Kunji fa menene ra’ayoyinku dangane da wannan batu?

Comments