Min menu

Pages

Zanga-zangar da za ayi yau abinda ya kamata mutane su sani idan ma da basu sani ba

 Game da zanga-zangar da za ayi yau abinda ya kamata mutane su saniAbinda ya kamata kowa ya sani game da zanga-zangar da wasu yan kudu ke shiryawa wanda za ayi yau asabat sha biyu ga wata kamar yadda zancen ya cika kafafen yada labarai. 


Da farko dai su a cewarsu za suyi wannan zanga-zangar ne domin a samu masalaha na wasu abubuwa da suke ganin an rasa a Nijeriya kamar tsaro da kuma rashin aikin yi ga matasa sannan da rashin tallafi daga gwamnatin Nijeriya kamar yadda suka ce..


Sannan sun sake cewa ana fama da tsadar rayuwa duba da yadda komai yai tashin goron zabi kama daga abinci da sauran kayayyaki..

Dan haka suka shirya wannan zanga-zangar don ganin an shawo kan wannan matsalar..

To amma a zance na hakika ko kuma mahanga ta hankali kowa yasan badan wannan matsalolin suka shirya wannan zanga-zangar ba sun shirya ta ne domin ganin cewa a dole sai Buhari ya sauka kamar yadda muke ji ta karkashin kasa ko kuma a raba kasar a ware musu tasu.


Dan haka yin wannan zanga-zangar bazai haifar da wani da mai ido ba duba da yadda akai asarar kayayyaki masu matukar yawa a waccen zanga-zangar da akai a baya..


Dan haka yanada kyau tun wuri a yiwa tufkar hanci kar a bari wannan zanga-zangar tai tasiri.


Allah ka kare mana kasar mu.

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment