Min menu

Pages

Matasan Arewa basu san ciwon kansu ba inji sowore saboda wannan dalilin

Matasan Arewa basu san ciwon kansu ba inji sowore saboda wannan dalilin
Matasan Arewa basu san ciwon kan su ba, mun yi zanga-zanga a yau amman babu shegen da ya taya mu~Inji Masu zanga-zangar kyamar Buhari a yau


Daya daga cikin masu zanga-zangar ganin an kifar da gwamnatin shugaba Buhari a yau mai suna Daniel Sunday ya kira matasan Arewa cewa basu san ciwon kan su ba, domin babu shegen da ya fito ya taya su zanga-zanga.


Daniel ya ce tun da har matasan Arewa basu san ciwon kan su ba su ma zasu hakura da yin wannan zanga-zanga su koma gida.


Daniel ya ci gaba da cewa" Ko lokacin da muka yi zanga-zangar ENDSARS haka matasan Arewa suka zura mana ido suna mana kallon mahaukata. Alhali muna yi ne don ci gaban kasa."  


Shi ma dai Sowore jagoran wannan zanga-zanga ya yi mamakin rashin fitowar matasan Arewa dudda irin lokacin da aka dauka ana kiran-kiranye kan wannan zanga-zanga.


Wanda yake rashin armashin wannan zanga-zanga yasa Sowore yin batan dabo tun da rana har kawo yanzu.

Comments