Min menu

Pages

Ku fito zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari ranar asabat kada kuji tsoron komai~ sakon sowore ga magoya bayansa

Ku fito zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari ranar asabat kada kuji tsoron komai~ sakon sowore ga magoya bayansa



Kada ku ji tsoron jami'an tsaro a ranar Assabar, ku fito a yi zanga-zangar kifar da Gwamnatin Buhari~Sakon Sowore ga magoya bayan sa


Shahararren mai neman ganin an kifar da Gwamnatin shugaba Buhari ta karfin tuwo kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2015 sannan mai gidan jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore ya sake tunatar da magoya bayan sa da su shirya fitowa a ranar Assabar a wajen zanga-zangar kifar da Gwamnatin Buhari.


Sowore ya gayawa magoyan bayan nashi cewa kada su tsorota da barazanar jami'an tsaro da akace za a jibgewa a ranar.


Sowore ya ce duk yawan jami'an tsaron da za a jibge baza su kai yawan su ba, saboda haka basu isa su yi wani abu ba.


A ranar Assabar ne dai ya shirya za a yi wannan zanga-zanga a sassa daba-daban na Najeriya ciki harda, Kano, Zaria, Kaduna, Damaturu, Abuja, da sauran wurare.


Adon haka Sowore ya yi kira ga matasan da su fito su kwaci 'yancin su koda kuwa za a kashe su ne.


To sai dai zuwa yau Alhamis matasa dayawa sun yi barazanar kin fita wannan zanga-zanga, sakamakon ikirarin da ya yi cewa zai bada kyautar Naira miliyan 10 ga duk wanda ya mari Buhari a yau a Lagos.


Matasan sun kira abin da Sowore ya yi da wuce gona da iri, a don sun gano cewa ba zanga-zangar neman 'yanci ne yake so a yi ba zanga-zangar tada fitina ce.


Comments