Min menu

Pages

Zamu Tsamo 'Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Kangin Talauci Ta Hanyar Azurta Su~ inji Buhari

 Zamu Tsamo 'Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Kangin Talauci Ta Hanyar Azurta Su~ inji BuhariShugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, sun kafa wani babban kwamiti mai karfin gaske wanda zai iya aikin tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga kan kangin wuya na talauci da suke ciki.

An kama wani jirgi makare da dalolin amurka a Kano

Shugaba Buhari ya bayyana hakan a ranar talata 22 ga watan Yuni 2021, lokacin da yake rantsar da kwamitin wanda zai fara aiki kowanne lokaci daga yanzu.


Buhari ya ce, "Tun da har kasar indiya ta azurta mutun miliyan 270, mu kuwa a Najeriya zamu tabbatar mun azurta mutun miliyan 100"


Shugaba Buhari ya ce, tun can farko gwamnatin shi ta talakkawa ce an kafa ta ne da zimmar yiwa talakkawa gata adon haka bai kamata abari talakkawan suna shan wahalhalun rayuwa ba na talauci.


Shugaban ya kafa kwamitin da zai tsamo 'yan kasar mutun miliyan 100 kan kangin talauci wanda yake dauke da gwamnoni 6 ministoci 8, zai fara aiki daga yanzu zuwa kowa ne lokaci.


Mi Zaku Ce?Comments