Min menu

Pages

Yanzu yanzu wata gada ta karye inda ake tunanin ta turmushe mutane da dama

 Yanzu yanzu wata gada ta karye inda ake tunanin ta turmushe mutane da damaAna fargabar cewa mutane da dama sun makale bayan ruftawar wata gadar sama da ake kan aikin ginawa a daya daga cikin manyan titunan Nairobi a Kenya.

Wadanda suka makale sun hada da ma’aikatan gine-gine da kuma masu sayar da kaya a gefen titi

Kafofin watsa labarai na cikin gida sun bayar da rahoton cewa, an riga an ceto akalla mutane hudu.

Akwai gagarumin cunkoso a yankin da yammacin yau, yayin da ayyukan ceto ke ci gaba.

Comments