Min menu

Pages

Sheikh Gumi: A yi sulhu da 'yan bindiga tun da ana shirin yi da 'yan IPOB

 Sheikh Gumi: A yi sulhu da 'yan bindiga tun da ana shirin yi da 'yan IPOBfitaccen malamin addinin Islama a Najeriya Shekh Ahmad Gumi ya sanar a wannan Litinin cewa idan har gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da 'yan kungiyar IPOB na yankin Igbo to ya kamata ta saurari tsarinsa na yin sulhu da 'yan bindiga a jihohin arewacin Najeriya. 


A cikin hirarsa da DW a wannan yammaci ya ce akwai fulani makiyaya fiye da miliyan tara a cikin daji kuma idan gwamnati ta ci gaba da yi musu ruwan bama-bamai, babu abin da za ta haifar in ba karuwar harin ramuwar gayya ba. Sheikh Gumi ya kuma shaida wa DW cewa sulhun nan shi ne zai kawo karshen daukar dalibai a makarantun arewacin Najeriya. Shin me za ku ce?

Comments