Min menu

Pages

Wannan shine sabon firaministan Isra'ila shin kunsan mugun nufinsa ga al'ummar musulmi?

 Isra'ila ta sake fadawa hannun wani babban bayahudeWannan shine sabon Firaministan haramcciyar Kasar Isra'ila bayahude Naftali Bennett wanda ya maye gurbin Benjamin Natenyahu


Naftali Bennett yana da ra'ayin rikau na addinin yahudanci da kuma kyamar Musulunci da Musulmai, sannan yasha alwashin kawar da Falasdinawa tare da kwace matsugunan Falasdinawa da birnin Qudus gaba daya


Yace zai fadada mamayar da Isra'ila takeyi har zuwa yankin Kasar Jordan da wani yanki a Syria wanda yace asalin yankunan na kakanninsu Yahudawa ne


Ya ayyana dakarun Falasdinawa Hamas a matsayin dakarun ta'addanci wanda suka cancanci hukuncin kisa, yace zai yake su da dukkan karfinsa, kuma wai har abada Falasdinawa ba zasu samu 'yancin Kasar su ba muddin yana raye a cewarsa


Naftali Bennett tsohon sojan Isra'ila ne, kuma tsohon Ministan tsaron Isra'ila, babban attajiri ne, yana da dukiya sosai wanda yace zai sadaukar wajen daukaka yahudu da yahudanci a duniya


Yaa Allah Ka kunyatashi kamar yadda Ka kunyata Benjamin Natenyahu, Allah Ka nuna masa Ka fishi isa da iko, Allah Ka sa ya zama sanadi na samun 'yancin Kasar Falasdinu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Comments