Min menu

Pages

Sun kone shi da ransa saboda ya saci charger waya

 Wasu fusatattun matasa sun kone  wani da ransa saboda ya saci charger waya Kamar yadda labarin yazo, kwanan wani ya kare saboda wutar da wasu fusatattun matasa suka banka masa saboda ya saci charger ta waya.


Majiyar ta rawaito cewar matasan sun kone saurayin ne da ransa saboda kawai ya saci charger waya..


Koda yake dama an fada mutanen dake unguwar sunata korafin cewa ana daukar musu kayayyaki da suka danganci wayoyi da kuma kwamfiyutocin su.


To sai a yau ne dai dubun wani ta cika inda matasan dake unguwar suka kamashi ya saci charger waya wanda hakan yasa suka sanya masa taya tare da zuba masa fetir suka sanya masa wuta suka kone shi.


Koda yake har yanzu dai ba'a tabbatar da sunan mutumin da matasan suka kone ba amma dai abin ya faru ne a unguwar Banada dake garin makurdi jihar Benue.Comments