Min menu

Pages

Idan yarinya ta kamu da kaunar saurayi zata dinga tambayarsa wadannan abubuwan

 Idan yarinya ta kamu da kaunar saurayi zata dinga tambayarsa wadannan abubuwan
Yau bangaren soyayya muka tabo saboda dama shi wannan gidan taba kidi ne taba karatu kusan komai muna kawo wa indai mun fahimci zai birge masu bibiyarmu..

Dake wannann gidan ya tara mutane kala kala samari da kuma magidanta mata da kuma maza, dan haka mukanyi bakin kokari ganin mun kawo abinda zai faranta ran kowa.


Yau soyayya zamu tabo kuma za muyi bayani ne kai tsaye ga masu yawan tambayar ta yaya ake ganewa idan mace ta kamu da kaunar saurayi? Shin akwai abubuwan da take ne da zai nuna budurwa tana son wani saurayi ko babu? Wasu daga cikin tambayoyin da muke yawan samu kenan..


To yau cikin ikon Allah zamu kawo wasu abubuwa da idan har budurwa tana yawan yima daya daga cikinsu babu shakka ta kamu da kaunar ka domin haka manyan masana a bangaren soyayya suka fada.


Dan haka ga wasu daga cikin abubuwan ko kuma tambayoyin da budurwa ke yiwa saurayi idan tana kaunarsa.


Tambaya ta farko da yarinya zata rika yima shine kanada budurwa, ko kuma tana cewa waye ce budurwar ka? Hakika idan yarinya tana fada maka to ma'abota soyayya sun fadi cewa yarinya ta kamu da kaunar ka.


Yawan son ta ganka ko kuma ku tsaya tare da ita wannan ma hanya ce wacce ake gane budurwa ta kamu da kaunar saurayi domin zata rika kawo masa ziyara ko tana yawan wuce wa ta inda take tunanin yana zama domin kawai ta ganshi ko kuma tayi magana dashi.


Aiko sakon gaisuwa duk lokacinda kaji budurwa tana yawan aiko maka sakon gaisuwa to wannan budurwa kaunarka ce fal a zuciyarta.Yima shidima a koda yaushe, duk lokacinda budurwa zata rika yima wasu shidimomi kamar aiki wanki ko guga to itama wannan kaunarka take..


Yawan kiranka a waya tana gaisar da kai, duk yayinda budurwa ta yawaita kiranka a waya tace kawai gaisar dakai ta kira tayi to kada ka raba daya biyu sonka take.


Idan tana yawan baka wani abu da take sayarwa kyauta ko ka bata kudin taki karba idan mai talla ce to wannan ma alama ce ta tana kaunarka.


Yawan kare ka a zance misali idan ana zance ko ana musu cikin abokanka ko nata idan tana wurin ta dinga kareka to wannan ma alamar so ce.


Idan a aji ne yima attendance idan baka zo ba ko wani assignment to wannan ma alamar kauna ce.

Anan zan dakata idan kuna son muci gaba kuyi mana comment da tambayoyinku.


Duniyar labari

Comments