Min menu

Pages

KE DUNIYA :-AN KASHE 'YAN GIDA DAYA SABODA SUNA MUSULMI

 AN KASHE 'YAN GIDA DAYA SABODA SUNA MUSULMIWani matashin 'dan ta'adda wanda ba Musulmi ba mai suna Nathaniel Veltman 'dan shekara 20 a Canada, yayi amfani da motarsa ya bi ta kan wadannan iyalan gida ya takasu da mota ya kashe su, su hudu,  sai 'dan autan gidan ne kadai ya tsira, laifin su kawai don sun kasance Musulmai


Sunayen iyalan gidan, Salman Afzaal shekarunsa 46, Matarsa Madiha Salman shekarunta 44, sai 'yar su babba sunanta Yumna Afzaal mai shekaru 15, sai dattijuwa mahaifiyar Salman Afzaal mai shekaru 74, wanda ya tsira 'dan autan gidan mai suna Fayez Afzaal mai shekaru 9 yana kwance a asibitiBayan da 'dan ta'adda Nathaniel Veltman ya aikata ta'addancin bai gudu ba,  'yan sandan Canada sun kamashi suka tafi dashi yana ta dariya yana fadin cewa burinsa na kashe Musulmai ya cika


Binciken 'yan sanda ya tabbatar musu da cewa Nathaniel ya aikata kisan ne saboda kawai yana kiyayya da addinin Musulunci, kuma a gobe Litinin za'a gurfanar dashi a kotu domin ya fuskanci hukunci

Karanta Wani abin mamaki cikin wata al'ada wacce uwa da ya suke auren miji daya

Anyi jana'izar mamatan a yau Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada


Muna rokon Allah Ya karbi shahadarsu,  Allah ya hada Nathaniel da dukkan bakin cikin duniya da na lahira Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Comments