Min menu

Pages

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Biya Miliyan 100 Sadakin Amaryarshi

 Shugaban Majalisar Dattawa Ya Biya Miliyan 100 Sadakin AmaryarshiDuk da ya ce Najeriya ta Talauce, Shugaban Majalisar Dattawa, Lawan ya bawa sabuwar matar da ya aura Naira miliyan Dari (N100m).


Duk ikirarin da yayi na cewa Najeriya ta Talauce kuma ya kamata taci gaba da ciyo bashi don daukar nauyin muhimman abubuwan more rayuwa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya bawa sabuwar matarsa, Zainab Algoni Abdulwahid Naira miliyan Dari.


Idan baku manta ba Sanata Ahmad Lawan ya auri Zainab a asirce a wani biki na musamman da aka yi a jihar Borno ranar Juma’a.


 

An daura auren mai a masallacin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh da ke Maiduguri.


 

An yi taron ne a asirce don kauce wa suka daga jama’a yayin da ake sa ran Zainab za ta koma Abuja a ranar Lahadi.


An kuma gudanar da karamin biki a gidan dangin amarya da ke Gwange 1 Ward, Malut Shuwa Street, Maiduguri.


Wata majiya da ke kusa da Zainab ta shaida wa Jaridar SaharaReporters a ranar Asabar cewa Shugaban Majalisar Dattawan ya ba ta kyautar Naira miliyan 100 ‘yan kwanaki kadan bayan an gabatar da su ga juna.


 

An ce amaryar ta sayi gidaje uku a cikin Maiduguri daga cikin kudin.


 

“Lawan da kansa ya ba ta Naira miliyan 100 bayan ya ga hotunanta. Kudin sun yi yawa har Zainab ta sayi gidaje uku a nan Maiduguri,” in ji majiyar.

Comments