Min menu

Pages

Buɗe Dandalin Batsa Da Nai A WhatsApp Da Facebook Ne Ya Sa Nayi Mafarkin Na Mutu, Har Ana Min Azaba". Cewar wata budurwa

 "Buɗe Dandalin Batsa Da Nai A WhatsApp Da Facebook Ne Ya Sa Nayi Mafarkin Na Mutu, Har Ana Min Azaba". Cewar wata budurwa



Wata baiwar Allah mai suna Safiyya, ta bayyana yadda tayi wani mummunan mafarki mai cike da tsananin firgitarwa, wanda duk mai imani idan yaji sai ya shiga tai-tayinsa, musamman ga mai yin mummunan aiki.


Safiyya ta bayyana wa Gidauniya Tv cewa “a daren jiya na kwanta bacci, amma tin da baccin ya kwashe ni, da farko dai nayi mafarkin an zare raina, wato na mutu, bayan an kaini kabarina an rufe ni, sai aka tayar da ni aka dunga yi min azaba. Gaba ɗaya hankalina, da ruhinna suka hasko min dandalin filin tashin Alƙiyama".

 

“Nau’i-nau’in azaba ake min, kuma aka ce min ba za a bari ba har sai aikin sharrin da na gina a lokacin da ina da rayuwata a duniya ya gushe sannan za a daina yi min azabar, to ni dai a iya rayuwata da nayi a duniya, na san cewa ban gina gidan giya ko caca, ko gidan mata ba, da dai sauransu".


”Sai aka ce min ai na bude dandalin batsa a WhatsApp da Facebook, inda ake amfani da su wajen turo hotuna da bidiyoyi na batsa a cikinsu, kuma ba za a daina yi min azaba ba har sai an rufe waɗannan dandalullukan, sai nace to a bani dama in koma duniya in ɗauki wayata in rufe sai a dawo da ni cikin kabarina, sai aka ce min ai idan an zo ba a komawa".


“Sai na fashe da kuka aka dinga yi min azaba, sai da aka ɗauki shekara guda ana min azaba babu dare babu rana, sai kwatsam naji an tsaya an daina yi min sai nace Allah ya gafartamin ne? sai aka ce a a ai an rufe group ɗin ne a yau, shiyasa azabar ta tsaya, saboda na bawa wata ƙawata admin, kuma lokacin da shiriya ta zo mata sai ta goge dandalin na WhatsApp da Facebook, shiyasa na samu saukin azabar".


”Ana cikin haka sai naji an kiran Sallar Asubahi, sai na farka a firgice naje nayi Sallah, bayan na dawo sai na buɗe data sai naga ashe ba a goge dandalin ba, nan take na goge su, sannan na share duk wani bidiyo da hotunan batsa da suke cikin wayata".


To kunji dai da fatan Allah ubangiji ya shirye mu shirin addinin musulunci, ganin yadda wannan al’adar ta buɗe dandalin batsa ya zama kamar gasa a tsakanin matasan wannan zamani muna fatan Allah ya tsaremu, masu yi kuma Allah ya shiryesu.


'Yan uwa wannan mafarki da baiwar Allah nan da ta yi wa azi ne, saboda haka akwai buƙatar a yaɗa shi zuwa sauran groups don mu amfana, kuma Allah zai bamu lada.

Comments