Min menu

Pages

Buhari bazai samu lafiya ba da gawarsa za'a dawo inji Nnamdi Kanu

Buhari bazai samu lafiya ba da gawarsa za'a dawo inji Nnamdi KanuKasurgumin dan ta'addar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara wato Nnamdi Kanu, ya bara a safiyar yau yana cewa shi fa babban burinsa shine ace Shugaba Muhammadu Buhari, ya mutu ko kuma an tsige shi daga mulki saboda babu abinda yake tabukawa kasar.


Nnamdi Kanu ya kara da cewa duk lokacin da dan arewacin Najeriya ke mulki sai an samu gagarumin koma baya ga tattalin arziki da tsaron kasar, saboda basu iya gudanar da mulki ba amma kuma sune ke yin kaka gida wajen dafe madafun ikon kasar.


Nnamdu Kanu dai ya shara wajen yin batanci da sukar shugaba Muhammadu Buhari da al'umar yankin arewacin Najeriya, saboda adawarsa da zaman kasar a matsayin dunkulalliya, inda yanzu haka yake jagorantar kungiyar IPOB mai fafutukar ballewa daga Najeriya da gwamnatin kasar ta haramta.


Comments