Min menu

Pages

SHIKENAN BOKO HARAM SUN SHIGA UKU

 BOKO HARAM SUN SHIGA UKURundinar sojin Nigeria ta tura wani jan gwarzo jajirtaccen mayakin soja Manjo Janar CG Musa jihar Borno a matsayin sabon Theatre Commander Operation Hadin Kai


Manjo Janar CG Musa a shekarun baya an taba kaishi Borno a matsayin Sector 3 Commander, ya fara jan ragamar yaki da gaske yana fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram, watansa uku kacal sai aka cireshi saboda rashin gaskiya don an ga yana da niyyar gamawa da ta'addancin Boko Haram


Alhamdulillah yanzu maigirma sabon shugaban sojojin Nigeria Manjo Janar Faruk Yahaya ya sake dawo da Manjo Janar CG Musa fagen yaki da Boko Haram, ba ma matsayin Sector Commander ba, an damka masa matsayin Theatre Commander Operation Hadin Kai, Maiduguri tana hannunsa gaba daya


Yanzu haka akwai kayan yakin da aka boye wanda ya kamata tuntuni a bawa sojojin kundunbala amma an hana, Manjo janar CG Musa yana zuwa yasa aka fito da makaman da aka boye aka rabawa kowace bataliya na sojoji


Muna rokon Allah Ya taimaki sojojin Nigeria, Allah Ya basu cikakken ansara akan annoba 'yan Boko Haram

Comments