Min menu

Pages

Dan shekaru 65 ya yi wa kishiyar uwarsa fyade a Jahar Ekiti

 Dan shekaru 65 ya yi wa kishiyar uwarsa fyade a Jahar EkitiWani Tsoho Dan shekaru 65 mai suna Durodola Ogundele ya yiwa Kishiyar uwarsa fyade wadda keda Shekaru 85 a Duniya.


Acewar sa hakan ya faru ne har sau biyu, a yayin da yaje yi mata maganin gargajiya na ciwon kafa.


Wannan al'amari ya faru a ranar 15 ga watan yuni, inda ya samu nasarar danne ta a dakinta, tare da aikata mata wannan mummunan aiki.


 Yan sandan jihar Ekiti sun yi nasarar cafke shi, jnda suke cigaba da binciken lamarin kafin a yanke masa hukunci.


 Acewar Jami'in Hulda da Jama'a na yan sandan jihar Ekiti Sunday Abutu, suna cigaba da gudanar da bincike kafin tura su kotu domin yanke mashi hukuci

Comments