Min menu

Pages

Magidanci Ya Kama Abokinsa Tsirara Gidansa A Dakin Matarsa A Garin Katsina

Magidanci Ya Kama Abokinsa Tsirara Gidansa A Dakin Matarsa A Garin KatsinaWani magidanci ya kama abokin sa tsirara yaje kwartanci gidan sa a Unguwar Modoji, nan cikin birnin Katsina (mun sakaya sunan su).


Shaidu sun tabbatar ma Katsina Post cewa wanda aka kama din aboki ne na kut-da-kut da wanda aka je ma kwartancin.


Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata da marece.


Mun samu labarin cewa kwarton ya dade yana neman matar abokin nasa amma ta ki bashi hadin har ma ta kai ga ta fadawa mijin na ta.


Sai dai mijin da farko bai yadda ba saboda ganin irin alakar da ke tsakanin su da abokin na sa har sai daga baya.

 

“Matar ta dade tana fadawa mijin nata cewar abokin sa yana yi mata maganganun banza har ma yana neman ta.


“Amma shi mijin ya musanta kalaman matar saboda kallon irin alakar abotar da ke tsakanin su”, inji wani abokin mutanen biyu da ya bukaci a sakaya sunan sa.


Abokin ya cigaba da shaidawa Katsina Post cewa “Ranar da dubun kwarton ta cika magidancin ne ya fadawa abokin nasa cewar yayi tafiya amma sai ya labe a cikin ‘ceiling’ sannan ya hada baki da matar sa akan ta kira kwarton kuma ta ja hankalin sa har ya cire kayan jikin sa.


“Hakan kuwa na faruwa sai magidancin ya fito daga maboyar sa sannan ya kuma yi kururuwa abokan sa suka shigo gidan inda suka kama shi tsirara”.


Haka dai suka yi ta bugun kwarton sannan suka lalata mashi mashin din sa roba-roba da ya je kwartancin da shi kafin daga bisani su kai shi a wurin ‘yan sanda.

 

Allah ya tsare mu daga mummunar kaddara. Comments