Min menu

Pages

Ko A Film Ban Taɓa Gani Ko Jin Irin Wannan Labariba😳🤔

 Ko A Film Ban Taɓa Gani Ko Jin Irin Wannan Labariba😳🤔Munje Kai Kudin Aure Mahaifin Yarinya Yace A Daura Auren Kawai Aka Ce Mishi Kudin Sa Rana Aka Kawo Sai Yace Mana Ai Wannan Ce Ranar, Kamar Wasa Dai Yanzu Labarin Dana Ke Baku An Nemi A Mayar Da Wannan Kudin Ya Zama Sadaki.


An Kira Ango A Waya Shi Ma Ya Amince An Daura auren Yau Da Daddaren Nan, Ana Shafa Fatiha Mahaifin Yarinyar Yace Mana Wanda Zai Iya Kawo Dubu Hamsin A Matasayin Na Gani Ina So Ai Zai Iya Bayar Da Sadaki, Sai Yace Mana Mu Jira Shi Yana Shiga Gida Kawai Sai Gashi Da Wata Yarinya Da Hijabi Da Nikabi A Fuskar Ta.


Yace Muje Zai Kai Yarinya Dakin Ta Da Kan Shi, Haka Muka Shiga Motar Mu Shima Ya Dauki Yar Sa A Motar Shi, A Hanya Ya Siyi Zabi Guda Uku Da Madara L& Z Muka Ci Gaba Da Tafiyar Mu, Muna Zuwa Gidan Su Ango Yace Ina Dakin Ango Yake Aka Nuna Mishi Daki A Zaure Kawai Ya Shiga Yasa Aka Kira Ango Yace Shi Ma Ya Shiga Haka Ango Ya Saki Baki Yana Kallo Yana Nukewa, Kawai Ya Tura Ango Ya Jawo Kofa Ya Rufe Tare Da Cewa Allah Ya Bada Zaman Lafiya Ya Kama Hanya Ya Fice Ya Bar Mu A Tsaye Muna Zare Idanu Da Rike Haba.


Yanzu Haka Dai Mun Dawo Gida Mun Bar Ango Da Amarya A Dakin Zaure, Gaskiya Munga Abin Mamaki A Rayuwar Mu, Allah Ya Sanya Alkhairi Ya Bada Zaman Lafiya kaji harkar girma.


Daga Abokin Ango

Comments