Min menu

Pages

Limamin Ka’aba mai tsarki ya ziyarci Gwamna Zulum, ga abinda yace masa

 Limamin Ka’aba mai tsarki ya ziyarci Gwamna Zulum, ga abinda yace masaLokacinda suka hadu yace muna kallon dumbin nasarorin da ka samu a jihar Borno.


 Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, wani malamin Saudiyya kuma daya daga cikin Limaman da ke jagorantar sallar jam’i a Masallacin Ka’ba (masallacin Al-Haram) da ke Makkah, ya kai ziyara ga Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kamar yadda majiyar Madubi-H ta ruwaito. 


 Ziyarar da aka yi da yammacin Laraba a gidan Gwamnati, Maiduguri.


 Imam Bukhari, wanda shi ne shugaban tsangayar karatun Larabci ga wadanda ba ‘yan asali ba a Jami’ar Ummul Qura da ke Makkah, ya je Maiduguri ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, Shugaban Gidauniyar Al-ansar da ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a Borno.  a wani wuri a cikin Maiduguri.

Comments