Min menu

Pages

Ku harbe duk wanda kuka samu yana kallon fina finan kasashen waje inji shugaban kasar koriya ta Arewa Kim jong un

Ku harbe duk wanda kuka samu yana kallon fina finan kasashen waje inji shugaban kasar koriya ta Arewa Kim jong unShugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bada umurnin kashe duk wanda aka samu yana kallon fina-finan kasashen waje ko kuma safarar su zuwa kasar sa


Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya kafa sabuwar dokar kashe duk dan kasar sa da aka samu yana kallon fina-finan kasashen yamma ko kuma sanya tufafi irin na kasashen waje wadanda bana kasar sa ba.


Hakama, shugaban ya bada umurnin kashe duk wanda aka samu yana mugun aski ko kuma yin wani yare na kasashen yamma.


Shugaban ya bayyana wadannan abubuwa a zaman wata guba da ka iya gurbata tarbiyyar ya'yansu da kuma al'adun kasar su.


Wata mata mai suna Yoon Mi-So ta bayyanawa bbc cewa a lokacin da take shekara 11 ta taba ganin an kashe wani mutun saboda ya yi wasan kwaikwayo irin na Koriya ta Kudu.


"An tara dukkan makwaftan mutumen sannan aka daure shi da igiya aka harbe shi".


"Idan kuma ka ki halartar kisan, za a kama ka da laifin cin amanar kasa, kuma kashe ka za a yi".


Shin ya kuke kallon wannan doka da shugaban Koriya ta Arewa ya kakabawa al'ummar sa ne?


Comments