Min menu

Pages

Tayi Nadamar shiga addinin musulunci bayan ta karbi kalmar shahada a watan Ramadan

 Tayi Nadamar shiga addinin musulunci bayan ta karbi kalmar shahada a watan RamadanCikin kowacce Shekara Musamman Acikin watan Ramadan Ana Samun Dabban Mutane Masu Yawan Gaske da suke Zuwa Majalisan Tafsirai  Domin karban Kalmar Shahada Akwai Wata Baiwar Allah Data taso Daga Kudancin Nigeria Tazo Arewa Domin karbar Kalmar Shahada Acikin Ikon Allah Wannan Baiwar Allah ta Musulunta Sai aka Nema Mata Taimakon Kudi Kamar Yanda aka Saba Ga Duk Mutumin Daya Musulunta Ana nema masa Taimakon Kudi Domin ya Dogara  da kansa Kasancewar koya Koma wajen Yan uwansa baza Su Taimaka masa ba Kasancewar yanzu ya fita Daga cikinsu kuma Abin Bautawarsu ba Daya bane   zasu iya taimakonsa ne Matukar zai kafirce ma,Ana yayi Ridda Wannan Baiwar Allah Aka nema Mata Taimakon Kudi bayin Allah suka Hada mata har sama da Naira Million biyu  Sai a kayi Rashin sa,a aka samu wani Munafiki Daga Cikin Musulmai ya Lallaba Yaje wajen Wannan Matar yace yana sonta da Aure ai kuwan ya Aureta Bayan Biki da wasu Yan kwanaki Sai mijin yace Mata ta bashi Wannan kudin ya Dada acikin Kasuwancinsa Ai kuwan ta Dauka ta bashi 
Abinda ya Fara Yi da Wannan Kudin Shine Karo Aure ma,ana Auro Mata kishiya ko nace Abokiyar Zama Sauran Kudin yaci banza yaci wofi A Haka Kudin suka Kare 
Bayan Kudin sun Kare sai ya sake ta 
Ai kuwan Matar Nan ta shiga Damuwa Budar bakinta tace Wallahi Da tasan Haka Musulunci yake Bata Shiga ba. 
Innalillahi Wa Inna ilaihi Raji un 
Duniya Ina Zaki damu 
Gaskiyar Magana ya kamata a Hukunta Wannan Mutumin Kuma Kotu tasa shi ya biya Wannan Kudin 
Domin Hakan zai iya sawa tabar Musulunci Sakamakon Wannan Abinda Wannan Munafikin yayi Mata 


Comments

1 comment
Post a Comment
  1. Allah ya sa dai Kuma ba kage kuka yi ba, Allah ya sa ba Yan Koren su bane ku din, ku fake kuci zarafin mutumci ta wannan hanyar, sannan ku fada mana waye Wanda ya aikata hakan a Ina yake Don mu tabbatar da abinda kuka fada sannan mu kwata Mata hakkin ta Kuma mu hukunta shi

    ReplyDelete

Post a Comment