Min menu

Pages

WATA AL'ADA:- Inda uwa da ya suke auren miji daya

 Wata al'ada mai abin mamaki kabilar da uwa da kuma ya suke auren miji dayaKasancewar duniya nada fadi tare da girma da yawa hakan yasa mutanen cikin duniyar suke da yawan gaske.

Kamar yadda mutanen keda yawa haka garuruwan da suke zaune suma suke da yawa, hakama kabilun dake raye cikin garuwan keda matukar yawa.

Idan an samu kabilu dole a samu yare da al'adu cikin kowacce kabila wasu su baka mamaki idan kaji labarin yadda suke gabatar da al'adunsu wasu kuma su baka haushi da takaici in kaji yadda suke gabatar da tasu.

Yau cikin wannan shirin a wannan gidan zan kawo muku wata kabila wacce uwa da ya kan aurar miji guda kuma suyi zaman aure tare.

Nasan mutane za su cika da mamaki tare da al'ajabi na jin yaya uwa da ya zasu auri miji daya? Wasu kuma za suce anya kuwa hakan zai iyu?

A wasu al'adar kam sam irin haka bazai taba faruwa ba koda a addinan ce to amma dake masu iya magana sunce abincin wani gubar wani..

A wani yanki na kasar Bangladesh su wannan al'adar suke idan mace tana da ya wanda har takai munzalin aure to ita ma idan bazawara ce to saurayin yar tata zasu hada su aura.


Ya kuke ganin abin?

Mun gode da ziyartar website din nan namu bangaren bada labari na mamaki akan abubuwan dake faruwa a cikin duniya.

Comments