Min menu

Pages

Kasar Saudiyya Ta Kashe Matashi Kan Laifin Da Ya Aikata Yana karami

 Kasar Saudiyya Ta Kashe Matashi Kan Laifin Da Ya Aikata Yana karami



Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum mai shekaru 26 bisa laifin da ta tabbatar ya aikata a lokacin yana ƙarami.


Hukumomin Saudiyya sun zartar da hukuncin kan Mustafa Al-Darwish a ranar Talata, kan laifin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama suka ce ana zargin ya aikata lokacin da shekarunsa na haihuwa basu wuce 17 ba.


Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya wanda ya tabbatar da zartar da hukuncin, ya ruwaito cewa an samu Al-Darwish da hannu a zanga-zangar nuna adawa da gwamnati da zummar kashe jami’an tsaro a tsakanin shekarar 2011 da 2012.


Tun a shekarar 2015 aka kama matashin wanda mabiyin mazhabar Shi’a ne kan zargin kitsa zanga-zangar ta’addanci kuma aka zartar masa da hukuncin kisa a shekarar 2018, inda a watan Mayun bana wa’adin daukaka ƙararsa ya ƙare.


Rahotanni sun bayyana cewa, an yanke wa matashin hukuncin ne duk da tabbacin da ƙasar ta bayar a bara cewa za a daina yanke wa ƙananan yara hukuncin kisa.


Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International, ta ce babu adalci a shari’ar yayin da danginsa suka ce ya janye amsa laifin da ya yi a baya kasancewar ya amsa laifin ne saboda azabtar da shi da aka yi.


“Sai kawai a kafafen watsa labarai na Intanet muka ji cewa an zartar da hukuncin a ranar Talata,” a cewar ƴan uwansa.


Kazalikaƴan uwansa sun ce an yanke masa wannan hukuncin ne kawai saboda wani hoto da aka gani a wayarsa da ya ci zarafin wani jami’in tsaron Saudiyya.

Comments