Min menu

Pages

INNALILLAHI WA'INNAN ILLAIHI RAJI'UN: Wani matashi ya sassara mahaifinsa da gatari a ranar bikin Iyaye ta duniya

 INNALILLAHI WA'INNAN ILLAIHI RAJI'UN: Wani matashi  ya sassara mahaifinsa da gatari a ranar bikin Iyaye ta duniya 


Karanta wannan:- jarumar fina-finan hausa Rahida mai sa'a zata auri wani

A yayinda 'yaya nagari ke bikin iyayensu ta hanyar sanya hotunansu da saya masu kyaututtuka, cen kuwa  a jihar Edo Yan sanda ne suka kama wani yaro dan shekara 13 mai suna Abubakar bisa zargin kashe mahaifinsa dan shekara 79 mai suna Malam Sariakhi Oronsaye yana cikin bacci.


Majiyar ta ruwaito matashin yayi amfani da gatari wajen sassara mahaifin nasa har ya mutu a ranar Lahadi da ta gabata a Egbon Estate dake garin  Evbuotubu, a Benin, babban birnin jihar Edo.


Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, SP Kontongs Bello dama a satin da ya gabata sai da margayi Oronsaye ya kai karar dan nasa ofishin yan sanda na Evbuotubu saboda yaron yana yi masa barazanar kisa amma kuma sai daga baya tausayin da da mahaifi tasa ya janye karar yace yansanda su bar yaron ashe kuwa zai je ya kashe shi.


Iyalai da yan'uwan wanda ake zargin sun ce bashi da wata lalura ta tabin hankali lafiyarsa garau.

Comments