Min menu

Pages

AN KAMA MAI TAIMAKON BOKO HARAM

 AN KAMA MAI TAIMAKON BOKO HARAMMayakan sojin Nigeria sun kama wani matashi mai suna Wida Kachalla wanda yake yiwa kungiyar Boko Haram ISWAP safaran kayan masarufi da leken asiri


Sojoji sun kama maciyin amanar ne a kasuwar Benishek, lokacin da Wida Kachalla ya tabbatar an ganoshi a kasuwar za'a kamashi, sai ya cire layin wayarsa ya saka a bakinsa ya taune ya hadiye, amma an karbi wayoyin hannunsa


Wato ya cinye layin wayansa domin kada a gano lambar wayoyin sauran abokansa da suke aikin cin amanar tsaron Nigeria tare, amma ya makara, domin an riga da an samu dukkan datas da ake bukata wanda yake kan system din da akayi tracking dinsa


Wida Kachalla yana da alaka na kusa da wani kasurgumin kwamandan ISWAP mai suna Modu Sulum 


Muna fatan Allah Ya cigaba da tona asirin masu taimakon ta'addanci a duk inda suke Amin

Comments